A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, kamar yadda aka tsara yau Talata, 7 ga Yuli, 2026 ita ce ranar bankwana da Shahidin Jagora da za a gudanar a birnin Qom, Ayatullah al-Uzma Jawadi Amuli (H) shi ne ya jagoranci sallar jana'izar Shahidin Jagora, Ayatullah al-Uzma Shahid Sayyid Ali Hussaini Khamenei (Q) tare da wasu daga cikin iyalansa, Shahid Dr. Misbahul Huda Baƙiri, Shahida Sayyida Bushra Hussaini Khamenei, Shahida Zahra Muhammadi Golpayeghani (yar wata 14) da kuma Shahida Zahra Haded Adel wadanda duk cikar su suka yi shahada sakamakon harin ta'addancin da gwamnatin Amurka da haɗin gwiwar Sahyoniya suka kai a gidan Shahidin Jagoran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Miliyoyin mutane ne suka cika Masallacin Jamkaran ba ko masakar tsinke domin yin bankwana da masoyinsu kuma jagoransu. Birnin na Qum ya shaida taron jana'izar da ba a taɓa yi ba a cikin sa.







Ra'ayinka